Fadar Shugaban Kasa ta musanta ikirarin da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi cewa an yi watsi da yankin Arewa a mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Fadar ta bayyana cewa akwai muhimman ayyuka da shirye-shirye da dama da ake aiwatarwa a yankin Arewa a halin yanzu.
Kwankwaso, yayin wani taron tattaunawa kan gyaran tsarin kundin tsarin mulki na 2025 da aka gudanar a Kano ranar Alhamis, inda ya yi gargadin cewa ana karkatar da dukiyar kasa zuwa yankin Kudu, wanda hakan ke kara talauci da rashin tsaro a Arewa.
A martaninsa da ya wallafa a shafinsa na X, mai ba Shugaban Tinubu ahawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya kalubalanci ikirarin Kwankwaso.
Tinubu bai mayar da Arewa saniyar ware ba – Martanin fadar shugaban Nijeriya ga Kwankwaso
-


