Jami’ar Port Harcourt (UNIPORT) ta karrama Ministan Abuja, Nyesom Wike, da Uwargidar Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, da wasu da Digirin Girmamawa (Doctor of Science).
gAn bayar da lambar ne a bikin cikar jami’ar shekara 50 da taron yaye dalibai karo na 35, ranar Asabar.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa sauran wadanda suka samu karramawar sun hada da: Tsohon gwamnan jihar
Katsina Aminu Masari, wanda shine Shugaban Hukumar TETFund, da Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa da sauransu.



