By Salisu Ado Sulaiman
Binciken jaridar Punch ya nuna cewa jam’iyyar APC na ci gaba da rajistar sabbin magoya baya a jihohi daban daban na Najeriya.
Wannan ya zo ne a yayin da jam’iyyar ke ci gaba da shirye shiryen tunkarar zaben 2027, inda rassan ta daga jihohi 11 suka sha alwashin bai wa Shugaba Tinubu kuri’u miliyan goma sha biyar domin ba shi damar zarcewa kan wa’adi na biyu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar barazanar siyasa daga bangarorin hamayya masu yunkurin kawar da ita daga mulki a shekarar ta 2027.
Sai dai yayin hira da gidan talabijin na Channels, sabon shugaban APC Nentawe Yilwatda ya bayyana shirin daukar tsauraran matakai domin ci gaba da inganta tafiyar jam’iyyar.



