Jam’iyyar hadaka ta ADC ta yi zargin cewa tsoron musgunawa daga gwamnatin tarayya ne ya sanya gwamnonin Najeriya ke shakkun shiga cikin tafiyar su.
Sakataren rikon kwaryar jam’iyyar na kasa Bolaji Abdullahi ne yayi wannan zargi a birnin Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Bolaji ya nuna damuwa da cewa har zuwa wannan lokaci babu wani gwamna mai ci da ya shiga cikin jam’iyyar hadakar ta ADC, yana mai bayyana cewa musgunawa tamkar munafurta da cin amanar yan Najeriya ne.


