By Salisu Ado Sulaiman
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya bukaci hadin kai tsakanin yan siyasa, yana mai cewa kasar za ta samu ci-gaba ne idan har suka cire son kai ko nuna bangaranci.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Akpabio ya yi wadannan kalamai ne wajen taron bikin yar gidan sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa kuma tsohon gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo.
Taron bikin ya samu halartar yan majalisun tarayya akalla guda 70, ciki har da kakakin majalisar wakilan Najeriya Tajuddeen Abbas.



