Salisu Ado Sulaiman
Babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zaman ta a jihar Legas, ta bai wa hukumar kula da masu yi wa kasa hidima NYSC umarnin barin mata su rika sa siket bisa dalilan da suka shafi addini.
Yayin da take yanke hukunci a ranar 13 ga watan Yuni, mai shari’a Hauwa Yilwa, ta ce tilastawa mata saka wando da hukumar ke yi ya saba wa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, na ‘yancin gudanar da addini da kuma mutunci.
Tun da farko dai, wasu mata da suka kammala yi wa kasa hidima su biyu, Ogunjobi Blessing da Ayuba Vivian ne suka shigar da karar hukumar a lokuta daban daban, inda mai shari’a Hauwa Yilwa ta yanke hukunci bai daya.



