Shugabar rikon kwarya ta jam’iyyar Labour Party, Sanata Nenadi Esther Usman, ta ce jam’iyyarta tana da shirin gyara kura-kuran da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ta tafka, wadda ta bayyana da cewa ta gaza matuka.
Yayin da take zantawa da manema labarai a jihar Kaduna dangane da abubuwan da ke gudana a cikin jam’iyyar LP, Sanata Nenadi ta bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da bada goyon baya ga jam’iyyar, tana mai cewa LP za ta ci gaba da zama sahihin zabi mai mayar da hankali kan talakawa, domin dawo da fata da martabar kasa.
A cewarta, gwamnatin APC ta “talauta ‘yan Najeriya fiye da kowace gwamnati a tarihin kasar,” inda ta bayyana halin rayuwa a kasar a yau da cewa “ba za a iya jurewa ba.”


