Tsohon gwamnan jihar Borno kuma jigo a jam’iyyar APC, Sanata Ali Modu Sheriff, ya bayyana cewa hadakar ADC ba ta da karko kuma za ta rushe nan da watanni uku.
Yayin wata hira da aka yi da shi a talabijin, Sheriff ya musanta jita-jitar cewa yana shirin shiga ADC, yana mai cewa: “ADC fa? Su da jam’iyyar ce? Ka ba su watanni uku, za su waste, domin kowa cikinsu yana son takarar shugaban kasa.”
Ya kara da cewa ADC ba za ta iya maimaita nasarar da APC ta yi a 2013 ba, saboda ba ta da gwamnoni, tsari ko tushen siyasa irin na APC.
Jaridar The Nation ta Ambato shi na cewa, yunkurin hada kai a ADC kawai taron ‘yan takara ne masu buri, ba tare da wata tsayayyar manufa ko hadin gwiwar da za ta iya kai su ga nasara ba.



