DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Manufofin tattalin arzikin Tinubu na sake farfado da darajar Naira – Dangote

-

Shahararren ɗan kasuwa a Afirka Aliko Dangote ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa manufofinsa da ke haifar da daidaito a kasuwar canjin kudi da kuma karfafa Naira.

Dangote ya bayyana hakan ne lokacin da ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Jumoke Oduwole, ta kai ziyara zuwa masana’antarsa ta Dangote Refinery da Fertiliser da ke Ibeju-Lekki, Legas.

Google search engine

Ya ce sabon tsarin “Naira-for-Crude” da dokar “Nigeria First” sun taimaka matuka wajen magance matsalar samar da danyen mai ga matatun cikin gida.

Dangote ya jaddada cewa sayen danyen mai da Naira zai taimaka wajen cika bukatun kasuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ya bayyana cewa karancin sauye-sauye a canjin Naira da Dala ya dawo da kwarin gwiwa ga masu zuba jari, kuma yana fatan Naira za ta kara karfi nan gaba kamar yadda jaridar Daily Tust ta ambato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara