Wazirin Katsina, Ibrahim Idah, ya bayyana cewa hare-haren ‘yan ta’adda sun ragu matuƙa a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman a jihar Katsina.
Da yake jawabi a taron haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da shugabannin Arewa, Idah ya ce Tinubu ya cika alkawarin yaƙi da bazuwar makamai, wanda hakan ke haifar da raguwar hare-hare idan aka kwatanta da shekarun baya kamar yadda jaridar Premium Times ta sanar.
Ya kuma buƙaci a karfafi rundunar tsaron sa-kai da makamai masu ƙarfi domin ƙarfafa tsaro, sai dai shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya ja kunne kan haɗarin hakan, yana mai ba da misalin wani kwamandan sa-kai a Borno da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da zuwa ofishin hukumar da mayaka fiye da 50.



