Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar 2025 da 3.2% a 2026.
Wannan sabon rahoto na World Economic Outlook da aka fitar a watan Yuli 2025, ya fi hasashen da aka yi a watan Afrilu na 3.0% da 2.7%.
IMF ta kuma kara hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya gaba É—aya zuwa 3.0% a 2025 da 3.1% a 2026, yayin da yankin Sub-Saharan Africa zai kai 4.0% a 2025 da 4.3% a 2026.
Sai dai, IMF ta shawarci kasashen yankin su dauki matakan gaggawa na gyaran tsarin mulki da hukumomi, duba da kalubalen tattalin arziki da suke fuskanta.



