Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta sanar da ranar 18 ga watan Agusta, 2025 a matsayin ranar da za ta fara sabuwar rijistar katin zaɓe a duk faɗin ƙasar.
INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 30 ga Yuli, inda ta bayyana cewa aikin rijistar zai gudana daga matakin jihohi zuwa kananan hukumomi a fadin Najeriya.
Hukumar ta kuma yi gargadi ga ‘yan Najeriya da ke yawan yin rajista fiye da ɗaya, da kuma wadanda shekarunsu bai kai na rajista ba, da su guji karya doka, tana mai cewa za ta yi amfani da sabbin hanyoyin zamani don gano masu karya doka don fuskantar hukunci.
INEC ta ce ta shirya tsaf wajen gudanar da aikin cikin gaskiya da bin ka’ida, tare da tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa ya samu damar yin rajista cikin sauƙi da adalci kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.