Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozomomi ta Nijeriya (NANNM) ta bayyana cewa kashi 90 cikin 100 na bukatunsu da suka gabatar wa gwamnati ba su da wata bukatar kudi.
Shugabar reshen jihar Cross River na kungiyar, Josephine Bassey, ta bayyana hakan ne yayin da take tsokaci kan yajin aikin gargadi na kwana bakwai da kungiyar ta fara tun daga ranar Laraba, 30 ga Yuli.
Da take zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Calabar ranar Alhamis, Bassey ta bayyana cewa yawancin bukatun nasu na da nasaba da mulki ne da kuma tabbatar da hukuncin kotu.
Kashi 90 cikin 100 na bukatunmu ba su da alaka da kudi – Ma’aikatan jinya masu yajin aiki a Nijeriya
-


