Majalisar tattalin arzikin Nijeriya ta amince da wani sabon tsari mai suna Renewed Hope Ward Development Programme (RHWDP) da zai mayar da hankali wajen bunkasa yankunan gundumomi 8,809 a fadin kasar.
Ministan tsare-tsaren kasafin kudi da tattalin arziki, Sanata Atiku Bagudu, ne ya gabatar da tsarin yayin taron NEC, inda ya bayyana cewa shirin zai karfafa tattalin arziki da nufin cimma burin samun habakar tattalin arziki har kashi 15 cikin 100 na yankunan kafin shekara ta 2030.
Ya ce a kowane gunduma za a tallafa wa a kalla mutane 1,000 da ke da aiki ko sana’a, yayin da manyan gundumomi mutane 2,000 za a karfafa wa.


