DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeLabaraiShugaba Tinubu ya amince da kashe Naira biliyan 712.3 don gyaran filin...

Shugaba Tinubu ya amince da kashe Naira biliyan 712.3 don gyaran filin jirgin saman Lagos

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 712.3 domin gudanar da cikakken gyaran filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos, a wani bangare na kokarin farfado da bangaren sufurin jiragen sama a karkashin shirin Renewed Hope Infrastructure Development Fund.

Ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa jim kadan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a Abuja ranar Alhamis.

Keyamo ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da za a gudanar da cikakken gyaran tsohon ginin filin jirgin tun daga lokacin da aka gina sa.

A cewarsa, za a kammala aikin cikin watanni 24, kuma yana daga cikin shirin sabunta muhimman ababen more rayuwa da suka hada da sabunta filin saukar jirage da fitilun sauka a Port Harcourt da za a kashe Naira biliyan 42.1bn, da jiha Kano da za a kashe Naira biliyan 46.3bn, sai Lagos da aka ware Naira biliyan 44.1bn, domin rage jinkirin saukar jirage da ke faruwa sakamakon yanayi mara kyau.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata