Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Nijeriya ta janye yajin aikin da ta fara, kamar yadda ministan lafiya, Farfesa Ali Pate ya tabbatar a yau Juma’a bayan wani taron sirri da shugabannin kungiyar.
Ministan ya bayyana wa manema labarai cewa an cimma matsaya tsakanin gwamnati da shugabannin kungiyar, wanda hakan ne ya sa aka dakatar da yajin aikin.
Sai dai shugabannin kungiyar ta ki yin wani bayani ga manema labarai bayan kammala taron.
Tun ranar 29 ga watan Yuli, 2025 ne kungiyar NANNM ta fara yajin aikin gargadi na mako guda saboda kin daukar mataki daga gwamnatin tarayya, bayan kungiyar ta mika wa gwamnati gargaɗi na kwanaki 15 tun daga 14 ga Yuli, 2025.
Ma’aikatan lafiya da ungozomomi a Nijeriya sun janye yajin aikin da suka shiga – In ji Ministan Lafiya
-


