Agushi, daya daga cikin sinadarin abinci a Nijeriya, na gab da kafa tarihi a matsayin abinci na farko daga Afirka ta Yamma da za a harba zuwa sararin samaniya, a wani bangare na binciken yadda abinci daga yankuna daban-daban na duniya zai iya jurewa tafiya da zama a sararin samaniya
Temidayo Oniosun, wanda ya kafa cibiyar Space in Africa, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi kai tsaye daga Cape Canaveral, jihar Florida, kusa da cibiyar sararin samaniya ta NASA.
Tun da farko an tsara a harba rokar da za ta tafi da shi ranar Alhamis, amma aka dage saboda yanayin guguwa. Sai dai an sake tsara harbar rokar zuwa ranar Jumu’a da misalin 4:45 na yamma agogon Nijeriya.
Agushi zai kafa tarihin zama sinadarin girki na farko daga Nijeriya da zai je duniyar wata
-


