DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Neja na shan suka bayan ba da umurnin rufe wani gidan rediyo a jihar

-

Wata sabuwa ta kunno kai a jihar Neja bayan da Gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyo na Badeggi FM da ke Minna, babban birnin jihar, lamarin da ya janyo cece-kuce da suka daga kungiyoyin ‘yan jarida da masu kare hakkin ‘yan kasa ciki har da Amnesty International.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim ya fitar, gwamna Bago ya bayar da umarnin a rufe gidan rediyon tare da kwace lasisin aikinsa da kuma binciko bayanan mamallakinsa, a yayin wani taron jam’iyyar APC da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya zargi gidan rediyon da tayar da fitina da tunzura jama’a kan gwamnati, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban gidan radiyon na Badeggi FM Abubakar Shuaib, ya mayar da martani ga wannan mataki, yana mai cewa ya kamata gwamnan ya bi hanyar doka wajen gabatar da korafe-korafensa, maimakon tura jami’an tsaro su tsoratar da ma’aikatan rediyon ko mamallakinsa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara