Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki gwamnatin Nijeriya kan yadda ta ci gaba da yin shiru tsawon shekara shida bayan bacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, ba tare da wani bayani ko bincike mai ma’ana ba.
Dadiyata, wanda malami ne a Sashen Harsuna na Jami’ar Tarayya Dutsinma, kuma fitaccen mai sharhi a kafafen sada zumunta daga jihar Kaduna, ya bace ne tun ranar 2 ga Agusta, 2019, bayan wasu da ba a san ko su wanene ba sun tafi da shi daga gidansa da misalin ƙarfe 1 na dare.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar, Isa Sanusi, Daraktan Amnesty International a Nijeriya, ya bayyana cewa rashin jajircewar gwamnati wajen gano inda Dadiyata yake ko binciken lamarin ya kara nuna hadarin da masu sukar gwamnati ke fuskanta a kasar.
Sanusi ya kara da cewa wannan lamari yana nuni da irin halin matsin lamba da ‘yan Nijeriya ke ciki wajen bayyana ra’ayoyinsu cikin ‘yanci, yana mai kira ga gwamnati da ta dauki mataki gaggawa domin fayyace gaskiyar lamarin tare da kare hakkin dan Adam a kasar.
Kungiyar Amnesty International ta caccaki gwamnatin Nijeriya kan shiru, bayan shekara 6 da batan Dadiyata
-


