Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Filato, Yakubu Dati, ya bayyana cewa ana matsa wa gwamnoni lamba su halarci bukukuwa da jana’iza maimakon su mayar da hankali kan ayyukan ci gaba.
Da yake magana da gidan talabijin na Channels, Dati ya ce wasu na amfani da irin waɗannan bukukuwa wajen auna nasarar gwamna, maimakon duban ayyukansa.
Sai dai ya jaddada cewa akwai gwamnoni da ke kokarin saukaka wa jama’a ta hanyar samar da muhimman ababen more rayuwa.
Ana auna kwazon gwamnoni ne ta hanyar halartar jana’iza ko daurin aure a Nijeriya – tsohon kwamashina daga jihar Plateau
-


