Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai yiwu a kawo sauyi a dukkanin fannonin ci gaban Abuja cikin shekaru biyu kacal ba, yana mai cewa hakan ba shi da tushe a zahiri.
Wike ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron tattaunawa da manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin, inda ya mayar da martani kan korafe-korafen da suka shafi gibin da ake samu a bangaren gine-gine, ilimi, lafiya da sufuri.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su fahimci cewa gudanar da gwamnati na bukatar lokaci da tsara abubuwa bisa fifiko.


