Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya bayyana cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar adawa ta PDP yanzu ya lafa, sakamakon ficewar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Wike ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a birnin Abuja a ranar Litinin, inda ya tofa albarkacin bakinsa kan ficewar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar daga jam’iyyar.
Sai dai Wike ya ce duk da cewa an samu sauƙi, har yanzu akwai wasu muhimman matsaloli da ya kamata jam’iyyar ta warware domin samun dawwamammen zaman lafiya.
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya kuma bayyana wasu sharudda da, in aka cika su, za su taimaka wajen dawo da cikakken zaman lafiya a jam’iyyar, ciki har da buƙatar tabbatar da sahihancin zaɓen shugabancin jam’iyyar na yankin Kudu maso Kudu.


