Jigo a jam’iyyar Labour Party, Abayomi Arabambi, ya ce ba za a yarda da alkawarin Peter Obi na mulki zango daya ba, duba da tarihin sauya jam’iyyarsa daga APGA duk da cewa ya sha alwashin zama a cikinta.
A cewar Arabambi a hirarsa da gidan talabijin na Channels, Peter Obi ya ce ba zai bar APGA ba, amma daga baya ya fice.
Saboda haka, ba za su yarda da ikirarin zango daya da yake yi ba.



