Jam’iyyar APC ta soki kalaman tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, inda ta ce cike suke da rashin gaskiya da ruɗani.
Felix Morka, mai magana da yawun jam’iyyar, ya bayyana hakan a wata sanarwa, yana mai cewa El-Rufai na ci gaba da nuna bacin ransa kan gazawarsa ta zama minista, yana amfani da harshen batanci domin ɓata wa gwamnatin Tinubu suna.
Jigon a jam’iyyar haɗaka ta ADC ya ce sake zaben Shugaba Tinubu tamkar rushe sauran haɗin kan Nijeriya ne.
A cewar APC, El-Rufai da abokan tafiyarsa a jam’iyyar ADC ba su da wata manufa sai girman kai da kishin kansu, kuma ba su da wata hanya ko shiri da zai fi nasarorin da gwamnatin Tinubu ke samu a yanzu, kamar yadda ake gani a fannin noma, wutar lantarki, fitar danyen mai, gina hanyoyi, sauƙin hauhawar farashi da tallafin karatu na NELFUND.



