Matatar man Dangote ta bayyana cewa farashin litar man fetur a masana’antar yana nan daram a ₦850, tare da karyata jita-jitar cewa an kara farashi ko kuma an dakatar da aiki.
Jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Anthony Chiejina, ya ce masana’antar na aiki yadda aka saba ba tare da wata matsala ba, tana samar da sama da lita miliyan 40 na fetur a kullum, tare da isasshen dizal (Automotive Gas Oil).
Ya kara da cewa sayar da Residual Catalytic Oil (RCO) lokaci-lokaci bangare ne na harkokin kasuwanci na yau da kullum, ba wata alama ce ta tsaiko ko rufe aiki ba, duk da rade-radin da ake yadawa kamar yadda rahoton gidan talabijijn na Channels ya ruwaito.



