DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Uwargidar shugaban Nijeriya ta ba da tallafin naira miliyan 110 ga iyalan ‘yan wasan Kano da suka rasu a hatsari

-

Uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da tallafin Naira miliyan 110 ga iyalan ‘yan wasan Kano 22 da suka rasu a mummunan hatsarin mota a watan Mayu.

Rahoton gidan talabijin na Channels ya ce kowane iyali ya samu Naira miliyan 5 ta hannun Victim Support Fund, wani shiri na gwamnati da ke taimaka wa waɗanda suka shiga cikin bala’i da matsanancin hali.

Google search engine

Fadar shugaban ƙasa ta ce wannan taimako na cikin shirin gidauniyar Renewed Hope na shugaban ƙasa Bola Tinubu, tare da nuna tausayawa da kulawa daga tsagin jagoranci.

‘Yan wasan sun rasu ne a kan hanyar Kano–Kaduna yayin dawowa daga gasar National Sports Festival a jihar Ogun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ciyo bashi bayan cire tallafin man fetur ba dai-dai bane – Sarki Muhammadu Sanusi II

Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya soki gwamnati bisa ci gaba da ciyo bashi duk da...

Dan Majalisar dokoki a Zamfara da jiga-jigai a PDP sun sauya sheƙa zuwa APC

Dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Maradun II ta jihar Zamfara, Hon. Maharazu Salisu, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC tare da wasu...

Mafi Shahara