Shahararren mawakin Afrobeats, David Adeleke (Davido), ya bayyana cewa ya kashe dala miliyan 3.7 kwatankwacin Naira biliyan biyar, da miliyan dari shida da sittin da bakwai, a shirye-shiryen bikin aure na fari da matarsa, Chioma, da za a yi a Miami wannan karshen mako.
Bikin zai kasance na uku ga ma’auratan, bayan na kotu a Maris 2023 da na gargajiya a Legas a Yuni 2024.
Taron zai sami halartar fitattun ’yan Najeriya, ciki har da Gwamnan Osun, Ademola Adeleke.
Davido da Chioma sun fara haduwa sama da shekara 10 da ta gabata, kuma sun fuskanci kalubale, ciki har da rasuwar dansu Ifeanyi a 2022, kafin su haifi tagwaye a 2023 kamar yadda gidan talabijin na Channels ya tattaro.