Jami’an EFCC sun kai samame a Green Legacy Hotel da ke cikin Olusegun Obasanjo Presidential Library a Abeokuta, jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin masu zamba ne ta intanet.
Rahotanni sun ce an kama sama da motoci ma su tsada 20 da wasu kayayyaki a daren Lahadi yayin wani biki.
Gidan talabijin na Channels ya ambato shugaban harkokin kasuwanci na Otal doin, Vitalis Ortese, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayyana cikakkun bayanai ba.
Mai magana da yawun EFCC na Lagos, Ayo Oyewole, ya ce bai da cikakken bayani kan samamen amma zai bincika.



