Kungiyar ‘yan fansho ta Nijeriya NUP ta ce jihohi hudu ne kacal cikin 19 na jihohin Arewa suka bi umarnin gwamnatin tarayya na biyan ₦32,000 mafi karancin albashi na wata-wata.
Da yake jawabi Yayin taron shiyyar da ya gudana a jihar Kaduna, shugaban NUP, Kwamared Mohammed Sali, ya bayyana lamarin a matsayin Rashin adalci ga tsofaffi da suka sadaukar da shekaru da dama na yi wa kasa hidima.
Ya ce jihohi hudu ne kawai ke biyan mafi karancin ₦32,000 daga cikin 19 a duk wata.
A cewarsa jihohi da dama har Yanzu suna biyan kasa da ₦3,000, ₦4,000, ko ₦5,000,kuma wannan ba daidai ba ne indai ba so ake a gansu akan titi suna yawo ba.
Sakataren kungiyar Alhassan Balarabe Musa, ya kuma yi Allah-wadai da banbance-banbance tsakanin kudaden fansho na ‘yan fansho da wanda ‘yan siyasa ke samu.



