Shugaban Sojojin Kasa na Nijeriya, Lt.-Janar Olufemi Oluyede, ya bukaci karin hadin kai tsakanin sojoji, bangaren shari’a da sauran masu ruwa da tsaki domin murkushe ta’addanci a Nijeriya.
A taron horaswa na makarantar doka ta sojoji a Zariya, Oluyede, wanda Maj.-Janar Ahmadu-Bello Mohammed ya wakiltaya ce aiki tare da musayar bayanai da mutunta doka ne kawai zai taimaka wajen dakile ta’addanci a kasar.
Lt.-Kanal Henrietta Longpoe ta jaddada cewa yakar ta’addanci na bukatar haɗin kan al’umma baki ɗaya, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta tattaro.



