DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamna Zulum ya nada sabon shugaban hukumar Alhazai ta Jihar Borno

-

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da nadin Farfesa Yakubu Yunusa Musa a matsayin sabon shugaban hukumar Alhazai ta jihar, inda zai maye gurbin Alhaji Mohammed Dawule Mainok.

Wata sanarwa daga mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Dauda Iliya, ta bayyana cewa Farfesa Musa, ɗan asalin karamar hukumar Shani, ya kasance gogaggen malami kuma mai kwarewa a shugabanci.

Google search engine

Kafin wannan mukami, Farfesa Musa ya jagoranci Cibiyar kasa da kasa ta kimiyyar Alkur’ani a jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu da ke Kano, sannan kuma Farfesa a fannin karatun Larabci.

Haka zalika, sanarwar ta ce ya kasance mamba a hukumar ilimin Larabci da tsangaya ta jihar Borno, tare da rike manyan mukaman ilimi da na gudanarwa a ciki da wajen jami’o’i.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara