Hukumar zaben Nijeriya INEC ta sanar da shirinta na gudanar da zabukan cike gurbi a mazabu 16 a jihohi 12 na Nijeriya.
Zaben zai gudana ne ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, a rumfunan zabe na mazabun da abin ya shafa.
A sanarwar da ta fitar, INEC ta bayyana dokokin kada kuri’a, inda ta jaddada cewa ‘yan kasa masu katin zabe na dindindin PVC ne kawai za su iya kada kuri’a.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa za a yi amfani da na’urar BVAS wajen tantance masu kada kuri’a.