Mace mafi tsufa a duniya, Ethel Caterham, ta cika shekaru 116 a ranar Alhamis, 21 ga watan Agusta, a ƙasar Burtaniya.
Caterham ta gaji kambun na mace mafi tsufa a duniya ne a bana, bayan rasuwar wata ‘yar Brazil, Inah Canabarro Lucas, wacce ta rasu a watan Afrilu tana da shekaru 116.
An haifi Caterham a ranar 21 ga watan Agusta, 1909, a ƙauyen Shipton Bellinger na kudu maso yammacin Ingila, shekaru biyar kafin barkewar yaƙin duniya na farko.
A cewar gidan da take zama a Surrey, an gudanar da shagalin zagayowar ranar haihuwarta cikin natsuwa tare da ‘yan uwanta.



