DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ana zargin ‘yar tsaron shago da satar Naira milyan 29, har ta kama wa saurayinta gidan haya a Neja – ‘Yan sanda

-

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ta kama wata yarinya mai shekara 23 da haihuwa, Sarah Ogbonna, bisa zargin satar kuɗi da wayoyi da kimarsu ta kai naira miliyan 29 daga shagon da take tsaro a Obasanjo Commercial Complex, Minna.

Kakakin rundunar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce bayan an kama wacce ake zargi, ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi, inda ta bayyana cewa ta dade tana daukar kayayyaki daga shagon tun daga shekarar 2023.

Google search engine

Rahoton ya nuna cewa daga cikin abin da ta yi da kudaden akwai biyewa saurayinta, Samuel Bello, wanda ya gudu kuma ta biya masa kudin haya da kuma sayen kayan daki a Minna.

Haka kuma ta rika tura wasu kudaden ga babbar, yarta Mercy Ogbonna don taimakon gidansu, da biyan haya da kuma siyan abinci.

‘Yan sanda sun kuma kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, ciki har da wata abokiyar aikinta Ruth Emmanuel wadda take cikin harkar kafin ta bar wurin, da kuma Nurudeen Musa wanda ake zargi da sayar da wayoyin da aka sata a farashi mai sauki.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara