DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sojojin Nijeriya sun yi ajalin ‘yan bindiga 7, sun kwato babura 4 a Katsina

-

Sojojin Nijeriya sun yi nasarar halaka ‘yan bindiga 7, tare da kwato babura a wani samame da suka kai kauyen Baba da ke Karamar Hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Katsina,Nasir Mu’azu, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Katsina.

Google search engine

Ya ce artabun da aka yi da ‘yan ta’addan ya dauki tsawon sa’o’i biyu a ranar Alhamis, 21 ga watan Agusta, 2024, bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’addan da ke addabar al’umman manoma a yankin.

Dakarun sojoji sun yi gaggawar kai farmaki inda suka fatattaki ‘yan bindigar, suka kashe bakwai daga cikinsu, sauran kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga, sojojin sun kwato babura hudu da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen aikata miyagun laifuka.

Ya ce wannan nasara na cikin ci gaban ayyukan sojojin da ake gudanarwa a kananan hukumomin da ke fuskantar barazanar tsaro, da nufin lalata mafakar ‘yan ta’adda da tabbatar da zaman lafiya domin inganta harkokin noma a wannan lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara