Fadar shugaban Nijeriya ta bayyana goyon bayanta ga tuhumar da hukumar yaƙi da rashawa ta ƙasa EFCC Abdullahi Haske, wanda surukin Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar kuma dan kasuwa a Nijeriya.
Haske, wanda shi ne mai kamfanin AA & R Investment Group, ya shiga jerin waɗanda EFCC ke nema ne bayan ya karya sharuɗɗan belin da aka ba shi, tare da gaza amsa gayyatar hukumar dangane da Zargin aikata laifi da almundahanar kudade da ake yi masa.
Jaridar Punch ta ambato cewa, majiyar EFCCin ta bayyana cewa Haske yana ƙarƙashin bincike tsawon watanni, sai dai bayan samun beli ya bace ba tare da bin ƙa’ida ba.
A cikin sanarwar da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, hukumar ta bukaci duk wanda ya san inda Haske yake ya sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma kowace cibiyar EFCC a faɗin ƙasa.
Sai dai kakakin Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, Paul Ibe, ya yi Zargin cewa an sanya siyasa a cikin binciken.



