Hukumar kula da kwalejojin ilmi ta Nijeriya ta gano tare da rufe kwalejojin ilimi 22 da ke aiki ba bisa doka ba a kasar.
Hukumar ta gano kwalejojin ilmi ne a lokacin wani samame da aka kai kan kwalejojin ilimi na bogi a faɗin kasar.
Wannan ci gaba ya fito ne a cikin jerin nasarorin da hukumar ta bayyana. Sai dai hukumar ba ta ambaci sunaye ko jihohin da makarantun suka fito ba.