Wani ɗan Nijeriya da ke zaune a birnin Dublin, na kasar Ireland, mai suna Stanley Abayeneme, na fuskantar shari’a bisa zargin kai wa maƙwabcinsa, Vilmantas Zutkis, hari bayan korafin cin zarafin wariyar launin fata.
A cewar rahoton jaridar Irish Sunday World, babbar kotun Dublin ta ƙi amincewa da buƙatar Abayeneme na neman wucin gadi don hana Zutkis ci gaba da yi masa kalaman wariyar launin fata.
Abayeneme, wanda ke gudanar da kasuwancin wanke motoci a yankin Tallaght, ya shaida wa kotu cewa Zutkis ya dade yana cin zarafinsa ta fuskar wariyar launin fata akai-akai.