Wani masani a fannin siyasa, Farfesa Jideofor Adibe, ya gargadi ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, Peter Obi, da ya yi taka-tsantsan da jam’iyyar adawa ta ADC, domin kada ya rasa damar tsayawa takara a 2027.
Da yake magana a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels, Farfesa Adibe ya ce manyan jam’iyyun PDP da APC sun riga sun karkata tikitin shugabancin ƙasa zuwa kudu, yayin da ADC ba ta bayyana matsayinta ba tukuna.
Ya kuma nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na nuna sha’awar tsayawa takara a 2027 a ƙarƙashin haɗakar ADC, abin da ka iya zama barazana ga ’yan kudu irin su Obi da Rotimi Amaechi.
Farfesa Adibe ya bayyana Obi a matsayin mutum mai zurfin tunani, amma ya jaddada cewa dole ne ya yi taka-tsantsan da shiri, yana kwatanta halin siyasar Najeriya da wasan catur wanda komai zai iya sauyawa a kowanne lokaci.