Kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya ASUU ta yi gargadin cewa za ta iya shiga yajin aikin gama gari, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen cika bukatunta.
Jaridar Punch ta ruwaito shugaban ASUU na jami’ar Akure, Farfesa Adeola Egbedokun ya na cewa har yanzu gwamnati ba ta aiwatar da yarjejeniyar 2009 ba, ba ta inganta ɗaukar nauyin jami’o’i ba, sannan akwai bashin albashi da matsalolin daga matsayin malamai da ake ta jinkirta wa.
Ya ce, lokaci ya kure, hakurin ASUU ya kai ƙololuwa, don haka ya roƙi majalisar dokoki, shugabannin addini da na gargajiya, tare da ɗalibai, su shigo lamarin dan gwamnati ta yi abinda ya dace.
Egbedokun ya yi gargadin cewa idan gwamnatin Tinubu ta kasa ɗaukar mataki bayan taron da aka shirya ranar 28 ga watan Agusta, to ASUU za ta ɗauki mataki mai tsauri wanda zai iya shafar makomar jami’o’in Gwamnati a fadin Nijeriya.