DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar ƴan sandan Delta na tuhumar jami’anta da karbar na goro

-

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Delta ta tabbatar da kama wasu jami’anta da suka bayyana a bidiyo suna lissafin dimbin kuɗi a cikin motar sintiri mai alamar Area Command Asaba.

Bidiyon ya bazu a shafukan sada zumunta, inda jama’a suka yi zargin cewa kuɗin na iya zama irin na goro da wasu jami’ai kan karba a manyan hanyoyi ko na kwace.

Google search engine

Jaridar Punch ta ruwaito mai magana da yawun rundunar, Bright Edafe, ya tabbatar da cewa an gano jami’an, an gurfanar da su gaban kwamishinan ’yan sanda, sannan an ɗauki matakin dakatarwa da tsarewa.

Ya ce tuni rundunar ta tura manyan jami’an biyu sashen tuhuma, yayin da sauran su biyun, masu mukamin Inspector kuma ake tsare da su don fuskantar shari’a a cikin gida, wacce ke matsayin tsarin ladabtarwa a rundunar.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Abin takaici ne ganin yadda Nijeriya ke cikin kasashen da talauci ya yi wa lahani – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana talauci a matsayin mafi girman maƙiyi da ɗan Adam ya taɓa sani. A cikin wata sanarwa da ya...

Nijeriya na iya shiga karin yanayin matsalar tsaro sakamakon karuwar yawan jama’a – Bankin Duniya

Shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, ya gargadi Nijeriya da sauran kasashen duniya cewa idan ba a dauki matakan gaggawa da hadin gwiwa ba, karuwar yawan...

Mafi Shahara