DCL Hausa Radio
Kaitsaye

ASUU reshen Jami’ar Sule Lamido a Jigawa, ta yi gargadin tafiya yajin aiki

-

Ƙungiyar malaman jami’a ta Najeriya ASUU reshen Jami’ar Sule Lamido, da ke Kafin Hausa, Jihar Jigawa, ta yi gargaɗin shiga yajin aiki idan har gwamnatin tarayya da ta jiha ba su warware matsalolin da suke tababa a kai ba.

A taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata, 26 ga Agusta, a ɗakin taro na tsangayar koyar da harkokin zamantakewa wato Faculty of Social and Management Sciences na jami’ar, shugaban ƙungiyar Dakta Mustapha Hussaini ya bayyana cewa jinkirin da gwamnati ke yi wajen sanya hannu a yarjejeniyar kungiyar da gwamnatin Najeriya da aka cimma tun watan Fabrairu na 2009, na nuni da cewa gwamnati na ƙoƙarin tura ƙungiyar ta koma yajin aiki.

Google search engine

Dakta Mustafa ya tabbatar cewa idan taron gwamnati da ake ƙoƙarin yi ranar 28 ga Agusta bai samar da wani sakamako ba, ASUU ba za ta bata lokaci ba wajen ɗaukar mataki mai tsauri.

Reshen ASUUn na Jigawa ya bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan matsaloli shi ne tilasta wa malamai shiga tsarin biyan albashi na IPPMS, wanda ya haddasa wa wasu malamai raahin albashi, rashin biyan kuɗaɗen kari da alawus-alawus, jinkiri wajen samun karin matsayi da albashi na shekara-shekara, da kuma jinkirin tura kuɗaɗen rancen ma’aikata zuwa asusun da ya kamata.

Ƙungiyar ta kuma yi korafi kan kin sakin Naira miliyan 604,719,866.14 da aka ware a kasafin kuɗin 2025 domin biyan bashin ƙarin albashin kashi 25% da 35%.

Haka kuma, ASUU ta zargi hukumomin jiha da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jami’ar, lamarin da ta ce ya sabawa dokar ikon gudanarwa na jami’o’i.

Reshen jami’ar ya bayyana cewa sun taɓa tattaunawa da gwamnatin Jigawa, ciki har da Akanta Janar, Shugaban Ma’aikata da Majalisar Dokokin Jiha, amma har yanzu ba a kawo ƙarshen matsalolin ba.

Shugaban kungiyar Garun-Gabas ya rufe da cewa ba za su ƙara lamunta ba irin wannan rashin kulawa daga gwamnati ba.

Suna kira a cire Jami’ar Sule Lamido daga tsarin biyan albashin hadin gwiwa domin gujewa katsewar karatu.

Ya ce yanzu aka fara gwagwarmaya!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Daga 2026 ₦500,000 kawai ɗan Nijeriya zai iya cira a banki cikin sati ɗaya – CBN

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake fasalin dokokin cire kuɗi daga bankuna kan sabon tsarin da zai fara aiki daga watan Janairun 2026. Babban bankin ya...

Ƴan kwangila sun girke akwatin gawa a ofishin ma’aikatar kuɗin Nijeriya

‘Yan kwangila sun girke akwatin gawa a kofar shiga ofishin ma’aikatar kudin Nijeriya da ke Abuja.   ‘Yan kwangilar, karkashin inuwar kungiyarsu ta 'yan asalin Nijeriya sun...

Mafi Shahara