Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce ziyarar aiki da Shugaba Bola Tinubu ya kai ƙasar Brazil na iya buɗe kofofin zuba jari sama da dala biliyan 30 a sassan tattalin arzikin Najeriya.
Da yake jawabi ga manema labarai a Brasília, Sani ya bayyana cewa yarjejeniyoyin da aka cimma a fannoni kamar noma, samar da abinci, jiragen sama da fasaha, za su iya sauya yanayin tattalin arzikin ƙasar.
Ya kuma ambaci sabbin yarjejeniyoyi a bangaren diflomasiyya, kirkire-kirkire da makamashi, yana mai cewa matakan da Tinubu ya ɗauka, musamman cike gibin dala biliyan 7 na canjin kuɗi, sun dawo da amincewar masu zuba jari ga kasar.
Gwamnan ya jaddada cewa goyon bayan ‘yan Najeriya ga shirin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu zai taimaka wa kasar ta tsaya da kafafunta kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta tattaro.