Mai magana da yawun hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS), A.S. Akinlabi, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Alhamis.
A cewar sa, an yi wannan gyaran ne domin tabbatar da inganci da amincin sabuwar fasfo ta Najeriya da za a fara amfani da ita daga wannan lokaci.
Sabbin farashin da aka kayyade sun haɗa da: Naira 100,000 ga fasfo mai shafuka 32, na shekara 5, da Naira 200,000 ga fasfo mai shafuka 64, na shekara 10.
Sai dai, kuɗin neman fasfo da ‘yan Najeriya da ke ƙasashen waje ke biya ba su canza ba, daga dala 150 ga mai shafuka 32, na shekara 5, zuwa dala 230 ga mai shafuka 64, na tsawon shekara 10.
Rahoton Jaridar Daily Trust ya ruwaito hukumar ta ce tana ƙoƙarin daidaita tsakanin ingantaccen tsarin aikinta da kuma samar da sauƙi ga ‘yan Najeriya wajen mallakar fasfo.