Bayan kammala zanga-zangar lumana a manyan jami’o’in Najeriya a ranar Talata, ƙungiyar malaman jami’a ta ƙasa (ASUU) ta sanar da cewa za ta gudanar da tarurrukan kwamitocin reshe a makarantu domin tattauna mataki n gaba.
A halin yanzu, gwamnatin tarayya na shirin ganawa da shugabannin ƙungiyar a yau domin tattaunawa kan yarjejeniyar da aka kulla tun shekarar 2009, wadda ita ce ta haddasa wannan zanga-zangar.
Tun farkon shekarar nan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta saki naira biliyan 50 domin biyan kuɗaɗen alawus-alawus ga malaman jami’a.
Sai dai ASUU ta jaddada bukatun ta na karin albashi, ingantaccen yanayin aiki, ‘yancin cin gashin kai ga jami’o’i, da kuma sake duba dokokin da suka shafi NUC da JAMB.