Rundunar ’yan sandan jihar Rivers ta bayyana cewa ta kwato ababen fashewa guda takwas da harsasai sama da dubu takwas, tare da kama mutum 33 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da ’yan bangar siyasa, masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da kuma masu safarar mutane.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kwamishinan ’yan sanda na jihar Rivers, Olugbenga Adepoju, ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron holen masu laifi a Port Harcourt a ranar Alhamis.
Ya ce an samu wannan nasara cikin watanni bakwai da suka gabata, musamman lokacin dokar ta-baci, tare da haɗin gwiwar sojoji, rundunar sojin sama da na ruwa, NSCDC, DSS da sauran jami’an tsaro.
Daga cikin wadanda aka kama akwai ’yan kungiyar asiri bakwai da ake zargi da ajalin wani lauya Bright Owhor a yankin D/Line na Port Harcourt.