Jam’iyyar APC reshen Jihar Legas ta bayyana cewa duk da girma da darajar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ba shi da karfin siyasa da zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta yi wannan bayani ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Seye Oladejo, ya fitar ranar Juma’a, inda ya mayar da martani kan jita-jitar da ke cewa Jonathan na iya tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Rahoton jaridar Daily Nigerian ya ambato Mr. Oladejo ya ce kalubalen da ake fuskanta a yau da gobe na bukatar shugabanci mai ƙarfin hali da hangen nesa, ba wai komawa ga abin da ya kira jiran gawon shanu ba.




Comment:Wai shin me Jonathan ya manta ne a villa?