By Fatima Aminu Dabo
Hukumar jin daɗin alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da jadawalin aikin Hajjin 2026, inda ta bayyana cewa 20 ga Maris, 2026 ce ƙarshe wajen fitar da visa, tare da jaddada cewa ba za a yi ƙarin lokaci ba.
A cikin sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce za a rattaba hannu kan yarjejeniyar shirye-shirye da hukumomin Saudiyya a watan Nuwamba, 2025, yayin da ta sanya 8 ga Oktoba, 2025 a matsayin rana ta ƙarshe ta tura kuɗaɗen jihohi da masu gudanar da hajji domin tabbatar da gurabe.
NAHCON ta yi kira ga hukumomin jihohi da kamfanonin jigilar mahajjata da su bi wannan jadawali don guje wa matsaloli, tare da tabbatar da hajji mai tsari da kwanciyar hankali ga ’yan Najeriya.



