Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana kwarin gwiwar cewa dokar ta-baci da aka ayyana a jihar Rivers za ta ƙare aiki a ranar 18 ga Satumba.
Wike ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa a zaben kananan hukumomi da ke gudana a jihar.
Ya ce ƙarewar dokar ta-bacin zai bai wa majalisar dokokin jihar damar ci gaba da gudanar da harkokinta na majalisa.
Ministan ya kuma bayyana cewa yanayi ya nuna dacewar cire dokar ta-bacin tun da gwamnati ta jiha da ta kananan hukumomi dukkansu suna da wakilci yanzu.

Dokar ta-bacin da aka kakaba a jihar Rivers za ta kare a ranar 18 ga watan Satumba, 2025, in ji Nyesom Wike
-
Comment:Kome nisan jifa kasa zata fadi