DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Zargin El-Rufa’i na gwamnatin Tinubu ta ba ‘yan bindiga kudin fansa, bai da tushe bare makama – NSA

-

Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya musanta ikirarin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya yi cewa gwamnati na biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga.

El-Rufa’i ya yi wannan zargi ne a gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.

Google search engine

Sai dai a wata sanarwa da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ta hannun Zakari Mijinyawa da ya fitar a Abuja ranar Litinin, ta bayyana wannan zargi a matsayin zargi marar tushe.

Mijinyawa ya ce wannan zargi da El-rufa’i ya yi bai da tushe balle makama, domin gwamnati na ta gargadin jama’a da kada su biya kuɗaɗen fansa saboda hakan na karawa ‘yan bindigar dama.

Ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki damarar yaƙi ta karfin soji tare da haɗa kai da al’umma, abin da ya kawo sauƙi a wasu sassan Kaduna.

A cewarsa al’ummomin Igabi, Birnin Gwari da Giwa, waɗanda da ke fama da hare-haren ’yan bindiga, yanzu sun fara samun zaman lafiya sakamakon irin kokarin da sojoji ke yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara